Ganduje Ya Danganta Cin Hanci Da Rashawa Kan Rashin Ingantattun Hukumomin Yaki Da Shi A Najeriya

ganduje

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr Abdullahj Umar Ganduje da Bishop Mathew Kukah sun danganta yanayin cin hanci da rashawa kan rashin hukumomi nagartattu na magance su a Najeriya.

Mutanen biyu sun bayyana haka ne a wani babban taro da shugabannin jam’iyyun siyasa na kasa da masu ruwa da tsaki suka gudanar a ranar Talata a Abuja, wanda TKC ta shirya.

A cewar Ganduje, Najeriya na bukatar kwararan cibiyoyi da za su yi aiki domin dora jam’iyyun siyasa da sauran jama’a da kuma taimakawa dimokradiyya a Najeriya.

Ya ce, “Babban matsalar da muke fama da ita a Najeriya ita ce ta raunanan cibiyoyi domin kawai muna tafka tafka ne gamida ta’asa, kuma babu hukumomi ingantattu na magance matsalolin.

“Sai dai idan ba muyi maganin wannan al’amari ba kuma muka ka sa sanya hukumominmu su yi karfi, muna zargin ‘yan siyasa ne kawai suke cin Karen su ba babbaka.

Jam’iyyun siyasa ma suna da matukar rauni kuma saboda wannan rauni, cin hanci da rashawa me cigaba da bunkasa.

“Kada mu rika zargin ‘yan siyasa, masu rike da mukamai, wadanda suka ci zabe, eh muna zarginsu, amma mu dubi tsarin tsaro, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), da ke kula da zaben.

“Wadannan cibiyoyi sun zama rumfunan zabe, don haka ku gaya mani, shin za ku iya lashe zabe kyauta? idan za mu yi cikakken bayani kan abin da ke faruwa a zahiri, za ku ga masu zabe suna cewa ba za su iya zabe ba har sai an biya su. .”

Anasa bangaren Mathew Kukah wanda ya jagoranci zaman taron yana mai kira da a yi koyi da kura-kurai da aka yi a baya domin karfafa cibiyoyi da dimokuradiyya a Najeriya a dukkan matakai.

Ya ce, “Ko bangaren shari’a ne ko na ofis, duk wani aiki ne da ake ci gaba da yi, kuma abu mafi muhimmanci shi ne mu koyi kura-kuran da aka yi a baya sannan mu samar da hanyar da za ta tabbatar da cewa abubuwa ba za su ci gaba da maimaita kansu ba. .

“Don haka, idan ka tambayi wanene ya gina cibiyoyin?, ya kamata cibiyoyi su zama madubi da ke nuna mahanga guda, da zata iya magance al’amuran tsaro, tabbatar da fata da kawar da damuwar al’umma baki daya.

“Hakan na nufin ‘yan sanda su zama cibiya, dole ne ‘yan Najeriya baki daya suyi koyi cewa a’a ga abubuwan da suka saba wa ka’idojin wannan cibiyar

Kukah ya yabawa kungiyar Tarayyar Turai bisa goyon bayan da take baiwa Najeriya wajen karfafa dimokuradiyya, musamman wajen bunkasa tsarin tafiyar da jam’iyyun siyasa (PPMT).

Wasu masu ruwa da tsaki a taron sun yabawa hukuncin da kotun koli ta yanke na baiwa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu.

Ya ce, “Hukumar PPMT ta bayyana cewa tasirin kudi a siyasa yana haifar da rashin jin dadi a dimokuradiyya da zabe.

“Kungiyar PPMT ta ba da shawarar shirye-shiryen bayar da tallafin gwamnati ga jam’iyyun siyasa don rage damar cin hanci da rashawa da kuma rage tasirin amfani da ‘jakar kuɗi yayin zabe.

“Har ila yau, ta ba da shawarar cewa jam’iyyun siyasa su inganta rikon sakainar kashi tare da bin tsarin gudanar da harkokin su batare da amfani da karfin iko ba wajan neman zabe .”

(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here