Wutar Lantarki ta hallaka mutane 5 tare da raunata wasu 13 a Gombe

Gombe State Map new 750x430

Rundunar ƴan sandan jihar Gombe, a ranar Asabar, ta tabbatar da mutuwar mutane biyar sakamakon kamun da wutan lantarki ta yi musu, yayin da wasu 13 suka samu raunuka a unguwar Tudun-Wadan Pantami dake cikin garin Gombe.

DSP Buhari Abdullahi, mai magana da yawun rundunar, wanda ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar yau Asabar.

Abdullahi ya ce, lamarin ya faru ne a sakamakon bindigar da na’urar taransifomar da ke kusa da su ta yi.

Ya kuma ce, da samun rahoton, jami’an ofishin ‘yan sanda kai ɗauki wurin domin tabbatar da tsaron yankin tare da kwashe wadanda abun ya shafa zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.

“Wadanda suka jikkata a halin yanzu suna samun kulawar likitoci a cibiyoyin lafiya daban-daban a jihar.

“An ajiye wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawa guda uku wanda suka haɗa da na asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya FTH Gombe da asibitin kwararru na jiha da kuma a dakin gawa na Bolari Filin Kwallo,” inji shi.

Abdullahi, a madadin kwamishinan ‘yan sanda, Bello Yahaya, ya jajanta wa iyalan mamatan tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.

Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa za’a gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin tare da tabbatar da bin diddigin lamarin yadda ya dace.

“Muna yi kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu tare da bayar da hadin kai ga kungiyoyin bayar da agajin gaggawa da masu bincike domin hana sake afkuwar wannan iftila’i a gaba.”

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here