Aminu Bala Madobi.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibrin ya kaddamar da shirin rabon tireloli 69 na takin zamani ga manoma a fadin kananan hukumomi 44 na jihar Kano.
An fara rabon tallafin ne a kananan hukumomin Danbatta da Makoda, da nufin tallafa wa manoman yankin, da inganta noma, da taimakawa wajen samar da abinci.
Shugaban ma’aikatan Sanata Barau, Farfesa Muhammad Ibn Abdallahi ne ya kaddamar da rabon kayayyakin, inda ya mika buhuna 2,804 da buhuna 1,910 ga al’ummar kananan hukumomin Danbatta da Makoda.
Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin sun yaba wa Sanata Barau bisa wannan karamcin da ya nuna, inda suka bayyana shi a matsayin shugaba mai fada da cikawa ga al’ummarsa.
Tijjani Yakubu Salisu, Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, ya godewa Sanata Barau bisa yadda ya ceci shirin noman su na gonaki, inda ya ce ya kasance yana nan a yankin Kano ta Arewa da kuma jihar Kano.
“Mun yi sa’a da samun shi; shugaba ne mai fada da cikawa ga al’ummarsa.
Sanatan mu ba shi da komai a zuciyarsa sai alkairi ga al’ummar Kano ta Arewa da Jihar Kano. Muna yi masa fatan alheri,” inji shi.
Yakubu Salisu, daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin daga karamar hukumar Makoda ya jin dadi yadda sanatan ya gwangwaje su da kayan inganta ayyukan noma.
“Wannan shi ne Sanata Barau a gare mu, yana yi mana tagomashi a koda yaushe, ba mu da bakin da za mu iya gode masa m, Allah SWT ya saka ma sa da alkairi, ya kuma biya shi, da yake iya share mana hawayen mu a koda yaushe.” Inji shi.