Kungiyar CISLAC ta nuna damuwa kan karin kasafin kudi na Naira tiriliyan 54.2

Civil Society Legislative Advocacy Centre CISLAC 1

Cibiyar kare hakkin jama’a da bibiyar ayyukan gwamnati ta (CISLAC) ta bayyana matukar damuwarta kan kudirin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na kara kasafin kudin shekarar 2025 daga naira tiriliyan 49.7 zuwa tiriliyan 54.2.

Kungiyar ta ce, tana sane da batun samun ƙarin ƙarin kudaden shiga daga manyan hukumomin gwamnati, wannan ne ya sa CISLAC ta ɗauki matakin a matsayin wanda ba a taɓa yin irinsa ba kuma mai yuwuwar sabawa tsarin mulki.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Auwal Ibrahim Musa (Rafsanjani), Babban Daraktan CISLAC, kungiyar ta yi tsokaci kan sashe na 81(4) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), wanda ya nuna cewa idan adadin da dokar kasa ta ware bai isa ba, ko kuma idan ana bukatar karin kashe kudi, dole ne a gabatar da karin kiyasi ga majalisar dokokin kasar.

Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa Rafsanjani wanda kuma ke rike da mukamin shugaban kungiyar masu fafutuka ta kasa da kasa a Najeriya, ya soki yadda aka bullo da karin kasafin kudin.

Karanta har ila yau: Taron Gwamnonin Tafkin Chadi ya zama abin koyi ga hadin gwiwar yanki-CISLAC

Maimakon bin tsarin da ya dace wajen yin ƙarin lissafin kasafin kuɗi, gwamnati kawai ta sanar da Majalisar Dokoki ta ƙasa ta hanyar wasiƙa, CISLAC ta yi gargadin cewa wannan bijirewa tsarin ka iya haifar da cikas ga gudanar da harkokin kasafin kudi a nan gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here