Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN ta zabi sabon shugaba

Most Rev Daniel Okoh emerges CAN President.v1
Most Rev Daniel Okoh emerges CAN President.v1

Kungiyar ta zabi Most Rev. Daniel Okoh a matsayin sabon shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN.

A wata sanarwa da Babban Sakataren kungiyar, Mista. Joseph Daramola, ya fitar a jiya Talata ne kungiyar ta sanar da samun sabon shugaban.

Wannan ya kawo karshen wa’adin shugabancin Samson Olusupo Ayokunle tare da ‘yan majalisar zartarwa na kasa karkashin jagorancinsa.

An haifi sabon shugaban, wanda dan asalin jihar Ribas ne, a Kano ranar 12 ga watan Nuwamba na shekarar 1963.

Okoh wanda ya yi makarantar Dennis Memorial Grammar School, ta Onitsha, ya kammala jami’ar Patakwal a shekarar 1988, inda ya samu digiri a fannin kimiyyar siyasa da Ilimi.

A yau Laraba ne kungiyar za ta fara babban taronta inda a lokacin za ta gabatar da sabon shugabancin, wanda zai karbi ragamar gudanarwa ranar Juma’a 29 ga watan nan na Yuli 2022.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here