Ana sa ran rage ribar Lamuni yayin da farashin kaya ke sauka – CBN

CBN CBN 750x430

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya ce akwai yiwuwar rage yawan ribar lamuni a ƙasar idan hauhawar farashin kaya ya ci gaba da raguwa tare da ingantuwar kasuwa.

Ya bayyana haka ne a taron Eurocham Nigeria C-Level Forum da aka gudanar a Legas a ranar Lahadi.

Cardoso ya amince cewa yawan kuɗin riba na hana saka jari sosai, amma ya ce matakan tsaurara kudin ruwa (monetary tightening) da aka ɗauka sun zama wajibi domin daidaita tattalin arziƙin ƙasa.

Ya bayyana cewa idan hauhawar farashin kaya ya ci gaba da raguwa, za a samu yanayi da zai ƙarfafa bayar da lamuni ga kamfanoni da kuma haɓaka zuba jari.

Karanta: Gwamnatin tarayya ta gayyaci Ɗangote da shugabannin NUPENG kan batun yajin aiki

Ya ce bankin ya ƙara kuɗin ruwa kwanan nan domin takaita hauhawar farashin kaya da kuma ƙarfafa Naira, kuma hakan ya fara nuna sakamako.

Cardoso ya kara da cewa babban abin da CBN ke mayar da hankali a kai shi ne tabbatar da daidaiton tsarin kudi da kuma ƙarfafa bankuna domin tallafawa ci gaban tattalin arziƙi.

Karin karatu: Kwastam za ta daina karɓar Haraji kan kaya ƙasa da dalar Amurka 300

Dangane da batun ƙara jari cikin bankuna (recapitalisation), Cardoso ya bayyana cewa ana samun ci gaba mai kyau, wanda zai haifar da bankuna masu ƙarfi da za su iya jure matsaloli.

Haka kuma ya ce haɗin gwiwar CBN da Ma’aikatar Kuɗi, Kasuwanci da Sanaa da Ofishin Kasafin Kuɗi na taimakawa wajen dawo da amincewar masu zuba jari.

Ya kara da cewa hauhawar farashin kaya ya na nan a matakin sama, amma yana raguwa sakamakon haɗin gwiwar da ake yi, kuma amfanin matakan tsaurarawar zai ci gaba da tasiri.

Ya kuma nuna cewa bunƙasar fasahar kudi (fintech) da kuma ƙarawa jama’a samun damar bashi za su taimaka wajen rage talauci da bunƙasa tattalin arziƙi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here