Majalisar wakilai ta yi gargadi kan yawan bashin da Najeriya ta fito da ya kai Naira Tiriliyan 149

Reps Speaker Abbass 720x430

Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya yi gargadi cewa bashin Najeriya ya kai wani mataki mai hadari wanda ba zai iya dorewa ba.

Ya bayyana hakan ne a wajen taron shekara-shekara na ƙungiyar West Africa Association of Public Accounts Committees (WAAPAC) a Abuja.

Abbas ya ce jimillar bashin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 149.39 (dala biliyan 97) a farkon shekarar 2025, inda bashin cikin gida ya kai kashi 53%, na waje kuma 47%.

Wannan ya nuna karin bashi sosai daga Naira tiriliyan 121.7 da aka samu a shekarar da ta gabata.

Ya kara da cewa yawan bashin da aka kwatanta da GDP ya kai kashi 52%, wanda ya zarce iyakar kashi 40% da doka ta tanada, alamar barazanar durkushewar tsarin kudi.

Karin karatu: Ana sa ran rage ribar Lamuni yayin da farashin kaya ke sauka – CBN

Ya ce idan ba a dauki matakan gaggawa ba, Najeriya na iya barin nauyin bashin a wuyan zuri’a masu zuwa.

Don haka ya jaddada muhimmancin sa ido daga majalisa wajen tabbatar da cewa duk wani aro ya kasance da gaskiya, tsabta da kuma amfani ga jama’a.

Abbas ya kuma bayyana cewa matsalar bashin ba ta tsaya ga Najeriya kadai ba, domin a nahiyar Afrika bashin ya kai dala tiriliyan 1.8 a 2022, inda kasashe da dama suka shiga hadari. Ya bayar da misali da Sudan (344%), Angola (136.8%), Ghana (84%), Kenya (70%) da Afirka ta Kudu (77%).

Ya ce a mafi yawan kasashe, kudaden da ake kashewa wajen biyan bashi sun fi na kiwon lafiya da sauran ayyukan jin kai.

Saboda haka ya bukaci a samar da tsarin duba bashin a matakin yanki, tare da karfafa kwamitocin majalisa masu kula da lissafin kudi domin su zama masu tsaron gaskiya da kiyaye al’umma daga bashi mara tushe.

Kakakin ya kuma nuna cewa yawancin bashin Afrika yana hannun masu ba da rance daga kasashen yamma (kashi 35%), Bankin Duniya da IMF (39%), yayin da kasar Sin ke da kashi 12 ne kacal.

Ya ce wannan tsarin yana sa kasashe su dogara da rancen waje mai tsada, wanda ke kara jefa tattalin arzikin nahiyar cikin hadari.

A karshe, Abbas ya ce Najeriya tana shirye ta jagoranci kafa tsarin kulawa da bashin kasashen yammacin Afrika a karkashin WAAPAC, tare da samar da bayanai na gaskiya da hanyoyin tabbatar da tsabtace lissafi. Ya jaddada cewa jama’a suna da hakkin sanin yadda ake cin bashi, kuma majalisa na da alhakin bayyana musu gaskiya

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here