TUC ta yi barazanar yajin aiki matukar gwamnati ta sanya harajin kashi 5% A kan Man Fetur

Pump price 1

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (TUC) ta yi watsi da shirin gwamnatin tarayya na sanya harajin kashi 5% a kan fetur, tana kiran wannan doka da “mugun shiri” da zai ƙara jefa ‘yan ƙasa cikin wahala.

TUC ta ce tuni al’umma ke fama da radadin cire tallafin mai, tsadar man fetur, hauhawar farashin kaya da faduwar darajar Naira, don haka ƙara wani sabon haraji zai ninka wahala, ya karya kasuwanci, ya kuma tura miliyoyin mutane cikin ƙarin talauci.

Kungiyar ta gargadi cewa gwamnati ba za ta ci gaba da amfani da ‘yan Najeriya a matsayin sikelin gwaji na manufofinta marasa tabbas ba.

Ta ce, “Maimakon samar da sauƙi da ayyukan yi, gwamnati na ƙoƙarin matse jama’a ta hanyar ƙarin haraji.”

TUC ta bukaci gwamnati ta janye wannan shiri baki ɗaya, tana mai jan kunne cewa idan aka ci gaba da shi, za ta shirya gagarumin yajin aiki tare da tursasa jama’a shiga zanga-zanga a duk faɗin ƙasa.

Karanta: Majalisar wakilai ta yi gargadi kan yawan bashin da Najeriya ta fito da ya kai Naira Tiriliyan 149

Shugabannin ƙungiyar sun umarci rassan TUC a jihohi da ƙungiyoyi mambobi su kasance cikin shiri, tare da kiran ƙungiyoyin farar hula, dalibai, kungiyoyin yan kasuwa da sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu su goyi bayan wannan gwagwarmaya.

A cewar TUC, lokaci ya yi da za a tsaya tsayin daka wajen hana manufofin da ke ƙara talauta al’umma, tana mai cewa: “Ya isa haka! ‘Yan Najeriya sun cancanci adalcin tattalin arziki, ba hukunci marar iyaka ba.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here