Ganawar sirri da gwamnatin tarayya ta shirya domin sasanta rikicin da ke tsakanin ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas (NUPENG) da kamfanin Dangote ta kare ba tare da cimma matsaya ba.
Ministan ƙwadago, Mohammed Dingyadi, tare da karamar ministansa Nkiruka Onyejeocha ne suka jagoranci zaman a kokarin hana yajin aiki da NUPENG ta shirya.
Babban batun rikicin ya ta’allaka ne kan batun shiga ƙungiyar kwadago da kuma wasu sharuɗɗa da Dangote ya yi ƙoƙarin sakawa a cikin yarjejeniyar fahimtar juna (MoU).
Rahotanni sun nuna cewa wakilan Dangote sun ƙara wasu abubuwan da aka bayyana da “cin fuska” ga ma’aikata idan har suka shiga yajin aiki, lamarin da ya sa tawagar NUPENG da NLC suka fice daga taron har sau biyu.
Dangote ya amince ma’aikatan sa na masana’antar mai da sinadarai su shiga NUPENG, amma batun sharuɗɗan da za a saka cikin yarjejeniyar ne ya kawo cikas. Wannan ya jawo saɓani mai tsanani tsakanin ɓangarorin biyu.
Zaman ya samu halartar wakilai daga hukumar kula da harkokin mai (NMDPRA), NUPENG, NLC, TUC da wakilan kamfanin Dangote.
A cewar wani ɗan ƙwadago da ya yi magana, har ma Dangote ya fice daga taron bayan bangaren ƙwadago ya dage cewa ba za a saka sharuɗɗan cin fuska ba a cikin takardar karshe.
NUPENG ta sanar a baya cewa za ta shiga yajin aiki daga ranar 8 ga Satumba domin nuna adawa da abin da ta kira yunƙurin Dangote na hana direbobin tankar iskar gas (CNG) shiga ƙungiyar.
Duk da cewa wasu ƙungiyoyin direbobi sun nesanta kansu daga yajin aikin, NUPENG ta jaddada cewa za ta ci gaba da shirin nata.
Gwamnati ta yi kira ga NUPENG da ta janye wannan yajin aiki saboda illa da zai yi wa tattalin arzikin ƙasa. Minista Dingyadi ya yi gargaɗin cewa ko kwana ɗaya na yajin aiki a ɓangaren mai zai haifar da asarar kuɗaɗe masu yawa da kuma jefa ‘yan ƙasa cikin matsanancin wahala.
Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da neman hanyar sulhu domin tabbatar da zaman lafiya a sashen man fetur.










































