Kungiyar tsoffin shugabannin jihohi na jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC) da ta gushe ta nesanta kanta daga ziyarar da wasu ‘yan cikinta suka kai wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.
Kungiyar ta bayyana wannan mataki a matsayin abin ruɗi da kuma wanda bai wakilci kungiyar gaba ɗaya ba.
Haka kuma, ta bukaci fadar shugaban kasa da shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da su gaggauta shawo kan abin da ta kira da ci gaba da nuna wariya ga bangaren CPC a jam’iyyar.
A wata sanarwa da suka sanya wa hannu Kasim Mabo shugaban jam’iyyar na ƙasa da Sulaiman Oyaremi sakatare na ƙasa kungiyar ta bayyana cewa daga cikin mambobinta 37, mutum 16 ne suka ayyana biyayya ga Atiku, yayin da mutum 20 suka ci gaba da kasancewa a APC tare da mara wa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu baya.
Sanarwar ta zargi shugabannin adawa da abokan Atiku da cewa suna matsa wa kungiyar lamba da alƙawarin kuɗaɗe domin janyo mambobi daga jam’iyyar mai mulki.
Ta kara da cewa wannan dalili ya sa wasu tara daga cikin mambobin suka hakura tun watanni da suka gabata, sannan guda bakwai suka biyo baya makon da ya gabata, inda yanzu mutum 20 kawai suka rage suna daurewa a jam’iyyar, bayan mutuwar ɗaya daga cikin mambobin daga jihar Borno.
Labari mai alaƙa: Tsoffin shugabannin CPC na jihohi sun ziyarci Atiku, sun sha alwashin mara baya ga ADC
Kungiyar ta kuma bukaci fadar shugaban kasa da shugabannin APC da su waiwayi irin rawar da CPC ta taka wajen kafa jam’iyyar, musamman kasancewarta a matsayin jigon da ya samar da gagarumin tsarin siyasa tun lokacin da ta hada gwiwa da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen samun kuri’un sama da miliyan 12.
Tsoffin shugabannin CPC sun bayyana cewa ziyarar da aka kai wa Atiku ba ta da wata ma’ana ta siyasa, illa kawai ƙoƙarin yaudara domin nuna cewa akwai goyon bayan da bai wanzu ba.
Sun ce taron ya kasance shiri ne kawai don jawo hankalin jama’a da yaudarar tsohon mataimakin shugaban kasa.
A ƙarshe, kungiyar ta sake jaddada goyon bayanta ga shugabannin tsohuwar CPC, ciki har da Sanata Umaru Tanko Al-Makura, Rt. Hon. Aminu Bello Masari da Rt. Hon, Tajudeen Abbas, tana mai cewa za ta ci gaba da nuna hakuri amma tana nan daram wajen neman kulawa daga shugabanci.
Sun yi addu’ar Allah ya ja-goranci shugaban kasa da sauran shugabanni a tafiyar da harkokin ƙasa.













































