Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a ranar Laraba ya karɓi tsoffin shugabannin jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC) da ta gushe, a gidansa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.
A shekara ta 2013, jam’iyyun CPC, Action Congress of Nigeria (ACN), da kuma All Nigeria Peoples Party (ANPP) suka haɗu suka kafa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Sai dai bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda shi ne ya kafa CPC, a watan Yuli, rahotanni suka nuna cewa wasu daga cikin mambobin jam’iyyar sun fara nesanta kansu daga APC.
Tun da farko a ranar Laraba, wani ɓangare na CPC da suka haɗa da Kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, da tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Tanko Almakura, sun ziyarci shugaban ƙasa Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa, inda suka yi masa alƙawarin mara baya a tazarcensa na 2027.
A lokacin tattaunawarsu da Atiku, tsoffin shugabannin CPC na jihohi sun bayyana kansu a matsayin “gaskatattun magoya bayan Buhari,” tare da sha alwashin mara baya ga haɗaɗɗiyar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ƙarƙashin jagorancin Atiku.
A cikin martaninsa, Atiku ya nuna kwarin gwiwa cewa ADC za ta yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 da goyon bayan tsoffin shugabannin CPC, inda ya ce za a kafa gwamnati mai tasiri wadda da maƙudan manufofin da Buhari zai so ya gani.
A wani rubutu da ya wallafa Atiku ya yi a shafin X, ya bayyana cewa tsoffin shugabannin CPC sun nuna damuwarsu kan yadda gwamnatin Tinubu ta kauce daga manufofin kare al’umma, wanda suka ce shi ne ginshiƙin farko na APC.
Ya ƙara da cewa ya yi bayanin yadda aka fara ƙoƙarin ƙirƙirar sabon haɗaɗɗen dandalin siyasa, yana mai ƙarfafa su da su tara magoya bayansu don rijistar zaɓe da ake yi yanzu.
Atiku ya bayyana jin daɗinsa da tattaunawar da ya yi da su, yana mai cewa yana sa ran haɗin kai mai ƙarfi da ba wai kawai zai kawar da gwamnatin APC ba, har ma zai dawo da sahihin fata ga ’yan Najeriya.













































