Kano: Sabbin ƙalubale sun hana kotu yanke hukunci a shari’ar yarinya ’yar shekara 14 da ake zargin fyade, daga baya aka tuhume ta da zina

Kano High Court

Babbar kotun jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Musa Ahmed ta dage zaman yanke hukunci a kan shari’ar wata yarinya da ake zargin dattijo mai shekara 65 ya yi wa fyade, bayan lauyoyin da ke wakiltar Babban Lauyan Jihar sun gabatar da sabbin buƙatu a gaban kotu.

A ranar Alhamis, tawagar lauyoyin gwamnati sun shigar da ƙalubalen farko kan ƙarar tare da gabatar da wasu takardu na ƙarin hujjoji, lamarin da ya hana ci gaban shari’ar kamar yadda aka tsara.

Saboda haka, kotu ta dage zaman don bai wa lauyoyin masu ƙara damar mayar da martani kan sabbin buƙatun da aka gabatar.

Kotun ta sake ɗage shari’ar zuwa ranar 8 ga Oktoba, 2025 domin yanke hukunci.

Shari’ar ta shafi Safara’u (Amira) Adamu, wacce yanzu ta kai shekara 16, wadda ta shigar da ƙara ta hannun mahaifiyarta kan Babban Lauyan Jihar Kano da kuma alkalin Kotun Majistare na Nomansland, tana ƙalubalantar shawarar da Ofishin Daraktan Gurfanarwa (DPP) ya bayar.

Karanta: Zargin Almundahanar Naira Miliyan 188.6: Hukumar yaki da cin hanci ta Katsina na bincikar kansiloli da malamai kan badakalar taki da kuɗin makaranta

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya fara ne a 2023, lokacin da ake zargin Mustapha Abdullahi daga unguwar Dansarai, ƙaramar hukumar Gezawa, ya yaudari yarinyar mai shekara 14 sannan ya yi lalata da ita a wani ginin da bai kammalu ba.

Daga baya, yarinyar ta ɗauki ciki ta haifi jaririya, duk da cewa an ce wanda ake zargin ya ba ta naira 500 don ta yi shiru.

Ko da yake an fara bincike a matsayin laifin fyade, daga baya DPP ya bayar da shawarar a sauya shi zuwa tuhume-tuhumen zina tare da gurfanar da yarinyar a matsayin wacce ake tuhuma tare da mutumin.

Wannan shawarar ta fuskanci ƙin yarda daga iyalan yarinyar da lauyoyinta, waɗanda suka bayyana cewa ƙarƙashin dokar Penal Code, ba za a iya gurfanar da yarinya ’yar shekara 14 da laifin zina ba.

A cikin rantsuwar da ta bayar, mahaifiyar yarinyar, Sakina Musa, ta yi zargin cewa an nuna son kai da rashin adalci wajen tafiyar da shari’ar, tana mai cewa shawarar DPP ta tauye adalci, ta jawo wa yarinyar cikas a karatu, kuma ta jefa iyalin cikin kunya da wariya.

Tawagar lauyoyin yarinyar na neman kotu ta bayar da umarni domin a soke shawarar DPP, tare da dawo da tuhumar fyade a kan wanda ake zargi a matsayin yadda aka fara.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here