‘Yan sanda sun kama mutane biyu a Kano bisa zargin fashi da makami a Legas

Police olopa new 750x430

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano ta sanar da cafke mutane biyu da ake zargi da hannu a wani sabon al’amari na fashi da makami da yunkurin kisa da ya auku a Jihar Legas.

Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna, ne ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar, inda ya ce nasarar ta samu ne sakamakon hadin kai tsakanin al’umma da karfin leken asiri na rundunar.

Sanarwar ta bayyana cewa a ranar 11 ga Satumba, 2025, jami’an musamman na rundunar sun samu nasarar cafke mutanen biyu a unguwar Na’ibawa dake Kano.

Wadanda aka kama sun hada da Mathew Adewole, mai shekara 25, mazaunin Na’ibawa, da kuma Mukhtar Muhammad, mai shekara 31, daga Unguwar Uku, Kano.

Karin labari: Kano: ‘Yan sanda sun kama sama da mutane 100 da ake zargi da aikata laifuka cikin sabon shirin “Operation Kukan Kura”

Bisa ga binciken farko, Adewole ya amsa cewa shi ne ya kai wa wani mai suna Lil-Kesh, mazaunin Bera Estate, Chevron, Legas, hari a ranar 19 ga Agusta, 2025, inda ya jikkata shi da raunuka masu tsanani, ciki har da yanka a wuya.

Bayan hakan, wanda ake zargin ya tilasta wa wanda ya ji rauni ya tura kudi naira miliyan biyu da dubu dari daya da ashirin (₦2,120,000) ta wayar salula zuwa asusun Mukhtar Muhammad.

Sanarwar ta ce bisa umarnin Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Kayode Egbetokun, rundunar ta dauki matakai na karfafa dabarun leken asiri da hadin gwiwa da al’umma domin kauce wa miyagun laifuka.

An mika wadanda ake zargi ga rundunar ‘yan sanda ta Jihar Legas domin ci gaba da bincike da gurfanarwa a kotu.

Kakakin rundunar ya kara da cewa, kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano, Ibrahim Bakori, ya yaba da kokarin jami’an rundunar da kuma hadin kan jama’a, tare da tabbatar da cewa za su ci gaba da daukar matakai don tabbatar da tsaro da doka a fadin jihar.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here