Wani kwararren likita a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano(AKTH) dake jihar Kano Dr Garzali lbrahim Umar ya yi kira ga sabbin shugabanin Najeriya dasu yi kokari wajan samar da likitocin da suka iya aikin hanta, yayin da kasar bata da likita ko da guda daya da ya iya wannan aiki.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa shugaban kwamitin tsara taron karawa juna sani akan aikin hanta wanda za’a gabatar da taron ranar Talata mai zuwa ne ya sanar da haka a yau Lahadi.
Ya kara da cewa akwai marasa lafiya da dama da suke bukatar aikin hanta kuma basu da kudin da za’a iya fitar dasu kashen waje domin aikin.













































