HOTUNA: Gwamnatin Kano ta cigaba da rushe gine-ginen da akai ba bisa ka’ida ba a jihar

FB IMG 1686471567140 1
FB IMG 1686471567140 1

Gwamnatin jihar Kano ta cigaba da rushe gine-ginen da akai ba bisa ka’ida ba, duk da sa bakin da shugaban kasa ya yi.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an rushe gine-ginen da ke filin wasa na Sani Abacha, da wadanda ke GSS Kofar Nasarawa kusa da titin IBB da kuma wadanda ke GGSS Dukawuya a Goron Dutse.

Shaidar gani da ido ya shaidawa Jaridar Solacebase cewa an yi rusau din ne a yau Lahadi da safe, wanda hukumar KNUPDA ta aiwatar bisa umarnin gwamna Abba Kabir Yusuf.

Idon zaku iya tunawa tsohon gwamnan jihar ta Kano Abdullahi Ganduje ya kai karar Sanata Rabiu Kwankwaso gurin Tinubu domin ya dakatar da rusau din da Gwamnatin NNPP take a Kano.

Haka zakilika shima Sanata Kwankwaso a nasa bangaren ya shaidawa yan jaridun fadar shugaban kasa cewa Tinubu ya kadu mutuka da ya shaida masa barnan da gwamnatin Ganduje tayi a Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here