Kotun Tarayya da ke Abuja, a ranar Laraba, ta dakatar da Babban Bankin Najeriya (CBN) daga ci gaba da sakin kasafin kudin wata-wata ga Gwamnatin Jihar Ribas.
Kamfanin dillacin labarai ta Najeriya (NAN) ta rawaito cewa wannan umarni ya shafi Akanta Janar na Tarayya (AGF), Bankin Zenith da Bankin Access, inda Gwamnatin Jihar Ribas ke ajiyar kudi.
Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, a hukuncinta, ta bayyana cewa karɓa da rabon kudaden wata-wata tun daga Janairun 2024 da Gwamna Siminalayi Fubara na Ribas ke yi, ya saba wa tsarin mulki kuma ba za a bar shi ya ci gaba ba.
Mai Shari’a Abdulmalik ta bayyana cewa gabatar da Kasafin Kudinsa na 2024 da Fubara ya yi gaban Majalisar Dokokin Jihar Ribas mai mambobi hudu ya zama wulakanci ga tsarin mulkin kasa.
Hakazalika, ta ce matakin da Fubara ya dauka na aiwatar da kasafin kudin da ba bisa ka’ida ba, ya zama wani salo na karya dokar kundin tsarin mulkin 1999 da ya rantse zai kiyaye.
A sakamakon haka, ta umarci CBN, AGF, Bankin Zenith, da Bankin Access da su dakatar da bai wa Fubara damar samun kudi daga Asusun Tarayya da Asusun Kasafin Kudi na Tarayya. (NAN)