
Wata Kotun Shari’a da ke Kofar Kudu a Jihar Kano ta bada umarnin tsare wani mutum mai suna Nasiru Mukhtar, bisa zargin cin zarafin wani limami a masallacin Tudunwada.
Rahoton ‘yan sanda ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne a ranar 22 ga Oktoba, 2024, misalin karfe 5 na safe, inda ake zargin Mukhtar ya iso wurin limamin, Malam Murtala Sulaiman, yana jagorantar sallar asuba, ya kama wuyansa, ya mare shi, ya yage masa kaya, kuma ya dauke makirifonsa.
Bayan faruwar lamarin, Malam Sulaiman ya kai rahoto ga Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano.
A cewar ‘yan sanda, zargin da ake masa ya yi daidai da sashe na 165 da 166 na dokar laifuka ta Jihar Kano.
A zaman kotun, wanda ake zargi ya musanta zargin.
Alkalin kotun, Malam Isah Rabi’u Gaya, ya ki amincewa da bukatar beli daga lauyan da yake kare Mukhtar, sannan ya bada umarnin a gudanar da gwajin kwakwalwa a asibitin gwamnati don tantance lafiyarsa.
An dage sauraron shari’ar zuwa ranar 22 ga Nuwamba, 2024, don ci gaba da bincike.