Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya dawo Abuja bayan kammala ibadar Umrah a Masallacin Harami dake Makkah, Saudiyya.
A wata sanarwa daga mataimakinsa kan harkokin watsa labarai, Stanley Nkwocha, an bayyana cewa Shettima ya yi addu’o’i na zaman lafiya da ci gaban Najeriya tare da jagorancinta a dukkan matakai.
Kafin tafiyarsa Saudiyya, Shettima ya wakilci Shugaba Bola Tinubu wajen kaddamar da wurin samar da mai da ajiya na Oriental Energy Limited da ya kai dala miliyan 315 a Dubai, UAE.