Ba zaki dawo aiki yanzu ba – Majalisar dattawa ta faɗawa Natasha

Natasha Akpoti 750x430

Majalisar Tarayya ta bayyana cewa dakatarwar watanni shida da aka yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga Kogi ta Tsakiya tana nan daram har sai kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan shari’ar da ke gabanta.

A wata wasika da mukaddashin sakataren majalisar, Dr. Yahaya Danzaria, ya aika wa Natasha a ranar 4 ga Satumba, an nuna cewa ko da yake sanatar ta sanar da niyyarta ta komawa aiki a wannan rana, dakatarwar nata ta fara aiki ne tun daga 6 ga Maris, 2025.

Saboda haka ba za ta iya ci gaba da aikinta a majalisar ba yayin da shari’ar ke gaban kotu.

Sanata Natasha ta kai kara kotun daukaka kara bayan kotun tarayya a Abuja ta yi hukunci a kan shari’arta da majalisar dattawa ta yi nasara.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here