Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Hukumar alhazai ta Najeriya NAHCON ta ce ta dauki dabarun rage yawan kwanakin da alhazan Najeriya ke yi a kasar Saudiyya yayin gudanar da aikin hajji.
Shugaban hukumar Malam Jalal Arabi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin da ta gabata yayin wata tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan ya isa filin jirgin saman Yarima Mohammed Bin Abdulaziz da ke birnin Madina.
Arabi ya bayyana cewa hukumar ta samu nasarar jigilar kashi 100 na alhazan Najeriya kai tsaye zuwa Madina.
Karin labari: ‘Yan sanda sun farwa masu garkuwa da mutane tare da kama wasu a Abuja
Sannan ya yabawa fadar shugaban kasa da majalisar dokokin kasar bisa gagarumin goyon bayan da suke bayarwa wajen samun nasarar ayyukan hajjin da ake gudanarwa.
Ya kuma yaba wa masu jigilar jiragen sama bisa yadda suke rayuwa.
Ya ce hukumar ta tanadi isassun tsare-tsare na ciyar da alhazai da kula da lafiyar alhazai a Masha’eer (lokacin ibadar hajji) wanda ake sa ran za a fara ranar 13 ga watan Yuni.
Karin labari: “Rufe wurin lantarki na kasa babban laifi ne” – Sakataren Gwamnatin Tarayya
A cewar shugaban hukumar NAHCON, ya kamata dukkan alhazan Najeriya su kasance masu hakuri da bin doka da oda da kuma shirye su yi ibada domin ba za a yi katobara ba.
“Daga abin da na gani a lokacin da na sauka a Madina, yanayi ya yi tsanani amma an gaya musu (alhazai) kuma an gargade su, kuma na tabbata sun shirya” kamar yadda NAN ta rawaito.