Hukumar DSS ta gano bindigogi da kakin Sojoji a gidan Tukur Mamu

ca76a0012e6a5abc
ca76a0012e6a5abc

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ce ta gano wasu kayyakin aikata laifuka da suka hadar da kayan sojoji, makudan kudaden kasashen waje a gidan mai shiga tsakanin wajen yin sulhu da ‘yan bindiga Tukur Mamu.

Mai magana da yawun hukumar ta DSS Peter Afunanya ne baiyana hakan ga Jaridar Daily Trust, a martanin da yayi kan sumamen da jami’an su suka gudanar a gida da ofishin Mamu ranar Alhamis.

Kazalika hukumar DSS ta ce ta gano kayayyakin laifi da dama, ta na mai cewa za ta gurfanar da shi a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here