Rugujewar gini ta yi sanadiyar mutuwar Yara 3 a Jigawa

Collapse building 750x430 1
Collapse building 750x430 1

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wasu yara uku bayan da wani gini ya rufta a karamar hukumar Dutse.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa ko da a ranar Lahadi ma rugujewar ginin ya halaka wata matar aure a karamar hukumar Gwaram ta jihar, bayan mamakon ruwan sama, a daren ranar.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Lawan Shisu Adam, shi ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa daya fitar a Dutse ranar Alhamis.

Shisu, ya ce lamarin ya faru ne da safiyar Laraba a unguwar Yakasai da ke kauyen Jigawar Tsada sakamakon ruwan sama da aka samu a yankin.

Ya Kara da cewa da samun rahoton faruwar lamarin jami’an ‘yan sanda sun isa wurin da lamarin ya faru, inda suka kwashe wadanda abin ya shafa sannan aka garzaya da su babban asibitin Dutse, daga nan Likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwarsu.

Mai magana da yawun rundunar ya kara da cewa tuni aka mika gawarwakin mamatan ga iyalansu domin yi musu sutura.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here