Mutane 10 sun mutu bayan da hatsari ya rutsa da su a babbar hanyar Jos zuwa Bauchi

FRSC FRSC
FRSC FRSC

Hukumar kiyaye aukuwar haddura ta kasa (FRSC) reshen Jihar Filato ta ce mutane 10 ne suka rasa rayukansu yayin wasu 15 kuma suka jikkata a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a kan babbar hanyar Jos zuwa Bauchi.

Kwamandan sashin, Alphonsus Godwin, shi ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a Jos, inda ya ce lamarin ya hada da wata babbar mota da wasu motoci guda shida.

Godwin ya ce wani direban babbar motar dakon kaya ya Kasa rike motar bayan da ta kwace.

Ya kara da cewa “Hatsarin ya haifar da cunkoson ababen hawa da ke shigowa da kuma fita daga Jos, amma jami’an mu na yin kokari wajen ganin sun sun Samar da sukuni a babbar hanyar.”

Godwin ya shawarci masu manyan motoci da su tabbatar suna kula da ababen hawansu yadda ya kamata, da sanya idanu akan direbobin su, sannan su daina daukar masu karancin shekaru a matsayin direbobi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here