Kungiyar malaman jami’o’i ta Kasa ASUU ta bayyana dalilan da suka sa ganawar ta da kwamitin gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Farfesa Nimi Briggs a ranar 16 ga watan Agusta ta kare ba tare da cimma matsaya ba.
Kungiyar ta bayyana cewa, tsaikon ya samo asali ne saboda wani tsarin albashin Malaman Jami’o’i na Consolidated University Academic Salary Structure (CONUASS) da aka ce hukumar kula da albashi da kudaden shiga ta kasa ta shirya mata.
Kungiyar, a cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta, Farfesa Emmanuel Osodeke, a ranar Alhamis, ta bayyana fushinta cewa “tsare-tsaren” da kwamitin Nimi Briggs ya gabatar ya zo ne a matsayin “ko a karba-ko-bari-shi”.
Shugaban na ASUU ya ce tsarin albashin, ya saba wa ka’ida dogaro da kundin dokokin ma’aikata ta 1 ta Shekarar 1973 da kundin dokar rikicin cinikayya ta Shekarar (1976).
Ya ce hakan ya sabawa yarjejeniyar ILO 49 (1948) da 91 (1950) da 154 (1988) da Kuma shawarwari 153 (1981) da Rahoton Kwamitin Udoji na Shekarar 1974, da Kuma Rahoton kwamitin Cookey na 1981.
A cewarsa, rahoton ya samar da hanyar warware muhimman batutuwan da suka hada da albashi na musamman da sharuddan gudanar da ayyukan ma’aikatan jami’o’i, da Samar wa jami’o’i kudade sai rawar da manyan shugabannin jami’o’i da hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) zasu taka.
Ya ce babban abin da aka samu shi ne tsarin albashi na musamman ga ma’aikatan jami’ar da aka fi sani da Tsarin Albashin Jami’a (USS).
Don haka ya ce, ya kamata Gwamnatin Tarayya ta hannun Ma’aikatar Ilimi ta dawo da daftarin yarjejeniyar da aka kulla karkashin kwamitin sulhu da aka kafa a Shekarar 2009, wanda aikinsa ya dauki tsawon shekaru biyar da rabi.
A cewar sanarwar, mai taken: “Me yasa ASUU ta ki amincewa da tsarin albashin da Gwamnati ta kawo”, kungiyar ta yi ikirarin cewa gwamnati ce ta haddasa masu yajin aikin da ake ci gaba da yi.













































