Kamfanin Sufurin jiragen sama na Emirates ya sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragensa zuwa Najeriya daga ranar 1 ga watan Satumbar Shekarar 2022.
Kamfanin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, inda ya ce ya kasa mayar da kudaden da ya samu a cikin kudaden kasashen waje daga Najeriya.
Idan dai za a iya tunawa, a watan Yulin Shekarar da muke ciki ta 2022, kamfanin Emirates ya nemi Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, da ya tallafa masa wajen dawo da kudaden shigar sa da suka kai dala miliyan 85.
Najeriya na fuskantar matsalar musayar kudaden waje hakan kuma ya shafi darajar kudin kasar wato Naira idan aka kwatanta da dala.
Kamfanin jirgin ya ce dakatarwar za ta “Kayyade karin asara tare da rage tasirin ayyukan sa da ke ci gaba a kasuwannin Najeriya”.
A watan Mayu, kungiyar sufurin jiragen sama ta kasa (IATA) ta koka kan gazawar kamfanonin jiragen sama na kasashen waje bisa gaza dawo da kusan dala miliyan 450 da aka samu a Najeriya.
















































