Ma’aikatan BDC sun bayyana dalilin daina ayyukansu a Abuja

ma'aikatan, BDC, ayyuka, bayyana, dalili
Ma’aikatan BDC sun sanar da rufe ayyuka a Abuja sakamakon rashin samun daloli. Shugaban kungiyar Malam Abdullahi Dauran ne ya sanar da hakan a babban...

Ma’aikatan BDC sun sanar da rufe ayyuka a Abuja sakamakon rashin samun daloli. Shugaban kungiyar Malam Abdullahi Dauran ne ya sanar da hakan a babban birnin tarayyar a ranar Laraba.

Dauran ya danganta ci gaban da kasuwancin kan layi da kuma cryptocurrency, ya ce rufe kasuwancin zai fara aiki a ranar Alhamis 1 ga watan Fabrairun 2024.

Karanta wannan: EFCC na binciken cinikin jiragen Najeriya – Minista

Wannan ci gaban dai na zuwa ne sa’o’i bayan da wani kwamitin majalisar dattawa ya gayyaci gwamnan CBN Olayemi Cardoso, kan rikicin saye da sayarwa.

Sanata Airu ya ce halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, musamman ma hauhawar farashin kayayyaki yana da matukar damuwa ga ‘yan majalisar.

Karanta wannan: Kotu ta dakatar da asusun Hisbah ta Jihar Kano

Ya ce: “Mun yi shawara a tsakaninmu. An dai tabo batutuwa masu muhimmanci kuma mun yi imanin cewa mataki na gaba shi ne a gayyaci gwamnan babban bankin kasar a ranar Talata da karfe 3 don ya yi mana bayanin yadda tattalin arzikin kasar ke tafiya yadda ya kamata.

“Wannan mun warware kuma za mu yi magana da gwamnan babban bankin kasa bayan haka za mu ci gaba da tattaunawa da ‘yan jaridu.”

Naira ta ci gaba da faduwa a ranar Talata, inda ta yi kasa da Naira 1,482.57 kan kowace dala, biyo bayan bukatar da ake yi a kasuwannin kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here