Kotu ta dakatar da asusun Hisbah ta Jihar Kano

Hukumar, Hisbah, Kotu, Dakatar, Asusu
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce an rufe dukkan asusun ajiyarta na banki biyo bayan karar da masu otal a jihar suka yi wa hukumar. Babban kwamandan Hisbah...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce an rufe dukkan asusun ajiyarta na banki biyo bayan karar da masu otal a jihar suka yi wa hukumar.

Babban kwamandan Hisbah Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya tabbatar wa da tashar TRT Afrika Hausa a ranar Laraba.

Idan dai za a iya tunawa a watannin da suka gabata ne jami’an Hisbah suka kai samame a wasu wuraren shakatawa a Kano lamarin da ya haifar da cece-kuce.

Karanta wannan: Abuja: ‘Yan Bindiga sun bukaci tallafin kayan abinci da Naira Miliyan 290

Daurawa ya ce, “Eh, gaskiya duk an kulle asusun bankin mu. Na aika da wakili ya gana da babban lauya saboda ba’a fada mana laifin da ake zarginsa da kuma dalilin rufe asusun ba.

“Mun samu takardar kotu da ke nuna rashin da’a a wasu otal guda biyu, wanda hakan ya sa aka tuhumi Naira Dubu 700,000 da Naira Dubu 100,000. Takardar ta bukaci a hada su a biya su Naira 800,000, lamarin da ya sa aka rufe asusun mu.

“Ya kamata a gaya mana laifin da muka aikata domin mu nemi lauyoyinmu su shiga cikin tattaunawar. Idan muka kasa kare kanmu, to za’a hukunta mu.”

Daurawa ya kuma nuna damuwarsa kan yadda hukuncin kotun ya gurgunta ayyukan Hisbah saboda takaita asusun ajiyar banki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here