Matatar man Dangote zata mayar da kudi ga yan kasuwar data sayarwa fetur da tsada

IMG 20240829 WA0005

Matatar Dangote ta ce, za ta mayarwa yan kasuwar da suka siya fetur a farashin daya zarce Naira 825, kan kowacce Lita kudaden su don saukakawa yan Najeriya.

A wata sanarwar da matatar ta fitar a karshen mako, ta ce mayar da kudaden zai saka matatar yin asarar Naira biliyan 16.

Idan za’a iya tunawa a makon daya gabata ne matatar man fetur ta Dangote ta sanar da rage farashin litar man fetur daga Naira 890 zuwa Naira 825 saboda a saukakawa yan Nijeriya a lokacin Azumin Ramadan, wanda matatar tayi makamancin wannan ragi a yayin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekarar 2025.

Labari mai alaƙa: Matatar Dangote ta sake karya farashin litar man fetur zuwa Naira 860 a Legas

Matatar ta kuma yi Allah wadai da yan kasuwar da take siyarwa da mai a farashi da sauki su kuma su tsauwalawa mutane farashin.

Matatar tace babu tausayi ga yan kasuwar da suke siyan man akan farashin naira 825, sannan su siyar a farashin Naira 945 ko sama da haka.

Matatar Dangote dai ta sanar da rage farashin litar man ta daga Naira 890 zuwa Naira 825, don alfarmar watan Ramadan, domin al’umma su samu sauki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here