Tsohon dan takarar gwamnan jihar Legas Jandor ya fice daga PDP

Jandor

Tsohon dan takarar gwamnan jihar Legas a jam’iyyar PDP Dakta Olajide Adediran, wanda aka fi sani da Jandor, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).

Jandor ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin sa na Ikeja da ke Legas a ranar Litinin 3 ga Maris, 2025.

Idan za a iya tunawa Jandor shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaben jihar Legas na 2023.

Kawo yanzu dai bai bayyana shirinsa na siyasa ba ko kuma dalilan ficewa daga jam’iyyar.

Karin karatu: Yanzu-yanzu: Kotun koli ta soke zaben ƙananan hukumomin jihar Rivers

Tun kafin ya koma PDP, Jandor ya kasance dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma ya jagoranci kungiyar Lagos4Lagos Movement, yana mai fafutukar tabbatar da dimokuradiyya a cikin jam’iyyar APC.

Jandor ya koma PDP ne a watan Janairun 2022 kuma ya samu tikitin takarar gwamna na jam’iyyar a zaben 2023.

A wancan zaben, ya zo na uku a bayan Gwamna mai ci Babajide Sanwo-Olu na jam’iyyar APC da Gbadebo Rhodes-Vivour na jam’iyyar Labour.

Ficewar Jandor daga jam’iyyar PDP ya kara dagula al’amuran siyasa a jihar Legas, wanda ke nuni da yanayin matsayarta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here