Farashin kayayyaki a Najeriya ya haura zuwa kashi 29.90 cikin 100 a watan Janairun 2024, a cewar sabon bayanan da Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ta fitar, ranar Alhamis.
Rahoton na NBS ya ce a cikin watan Janairun 2024, farashin kayan masarufi ya karu zuwa 29.90% idan aka kwatanta da hauhawar farashin kayayyaki a watan Disamba na shekarar 2023 wanda ya kai 28.92%.
Hakan na nufin cewa hauhawar farashin kayan masarufi a watan Janairun 2024 ya ƙaru da maki 0.98 cikin 100 idan aka kwatanta da farashin Disambar 2023.
Karanta wannan: Tinubu ya gana da gwamnoni kan taɓarɓarewar tattalin arziƙi da tsaro
Hakazalika, a kowace shekara hauhawar farashin kayayyaki ya kasance da kaso 8.08 sama da adadin da aka rubuta a watan Janairun 2023, wanda ya kai kashi 21.82 cikin 100.
A cewar NBS, hauhawar farashin abinci, a duk shekara ya kai kashi 35.41 cikin 100 wato da maki 11.10 cikin 100 idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Janairun 2023.
“Samun ƙarin farashin kayan abinci a kowacce shekara na faruwa ne sakamakon hauhawar farashin burodi da hatsi da dankali da dawa da mai da kifi da nama da ‘ya’yan itatuwa da dai sauran su.” in ji hukumar a rahotonta.