Daga: Halima Lukman
Dangane da yanayin da duniya ke ciki, Najeriya na fuskantar hauhawar farashin kayayyakin abinci da ba a taba yin irin shi ba.
Binciken da NAN ya fitar a jihohin Kaduna da Kano da Katsina ya nuna cewa Najeriya ba ta bar baya da kura ba.
Haka zalika, a wani bincike da manema labarai suka tabbatar a Kaduna ya nuna cewa an samu karuwar farashin shinkafa, burodi, sikari, gari, naman sa da kwai da dai sauran su, wadanda su ne abin dogaro a wasu gidaje.
Karin labari: ‘Yan Bindiga sun sace wani Hakimi a Kaduna
Har ila yau, hauhawar farashin ya yi tasiri a cikin yanayin rayuwa saboda yawancin gidaje yanzu suna ganin yana da matukar wahala a samu cin abinci sau uku a rana.
Farashin shinkafa mai kyau ya tashi zuwa kusan Naira Dubu 75,500 na kowanne buhu, yayin da mafi kyawun samfuran yanzu ana sayar da su daga Naira Dubu 77,000 zuwa Naira Dubu 80,000 dadai sauran kayayyakin masarufi.
A halin da ake ciki, manoma a sassan jihar sun danganta tsadar kayan abinci da cire tallafin man fetur.