Karancin Man Fetur ya kunno Kai a Arewacin Najeriya yayin da IPMAN ta Dakatar da ayyukanta

Pump price 1
Pump price 1

Karancin man fetur dai na kara kunno kai a babban birnin tarayya Abuja da Kaduna da Nasarawa da Kogi da Neja da sauran jihohi yayin da kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN reshen Suleja ta sanar da yajin aikin gargadi na kwanaki uku.

Shugaban kungiyar, Alhaji Yahaya Alhassan, wanda ya sanar da dakatar da ayyukan Kungiyar, ga manema labarai yayin wani rangadi da ya yi a inda aka ajiye motocin dakon man a Maje dake Suleja a Jihar Neja.

Mambobin Kungiyar dai sun dage cewa za su janye ayyukansu har sai gwamnatin tarayya ta biya kudaden da suke bi bashi da ya kai Naira biliyan 50 da doriya.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa reshen ke yajin aikin sai ya ce: “Asusun samar da daidaito a harkokin man fetur (PEF) bai biya mu kudaden mu ba.

Muna bin sana Naira biliyan 50 saboda haka mun janye ayyukanmu.”

Yajin aikin wanda aka fara a ranar Litinin zai ci gaba har zuwa ranar Laraba.

Idan har hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa (NMDPRA) ta gaza fitar da kudaden, yajin aikin zai ci gaba da gudana har sai Baba ta gani, in ji Alhassan.

Ya ce: “Wannan yajin aikin na kwanaki uku ne. An fara (daga ranar Litinin) zuwa (ranar Laraba).

Bayan haka, idan gwamnati ba ta biya mana bukatarmu ba, za mu ci gaba har sai abinda hali ya yi.”

Shugaban ya lura cewa duk koken da kungiyar ta yi wa hukumar kan biyan basussukan da suke bi an yi musu shakulatin bangaro.

“Mun zauna da shi (Babban Jami’in Hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed) sau da yawa kuma bai dauki Wani mataki a Kai ba. Bayan haka kuma, bai kira mu ba,” inji shi.

Sakataren kungiyar, Shu’aibu Muhammad, ya ce rumbunan ajiyar man dake arewacin Najeriya guda tara sun shiga yajin aikin gargadin.

Ya bayyana cewa, tare da hadin kai da Depot na Suleja, sauran gidajen man da ke yankin sun janye ayyukansu.

Muhammad ya jaddada cewa idan Ahmed ya ce ya biya sama da Naira biliyan 74 a cikin watanni bakwai, “gwamnati ta biyan wani abu amma ba ta biya abin da ya dace ba.”

Ya kalubalanci hukumomi da su gabatar da shaidar da ke nuna cewa an biya ’yan kasuwar kudin dakon su.

A kwanakin baya hukumar NMDPRA ta yi ikirarin cewa ta biya kimanin Naira biliyan 74 ga ’yan kasuwar, inda ta jaddada cewa wadanda ke korafin suna bin bashi zantuka ne da ba su da tushe.

A cewarsa, ’yan kasuwar da suka fusata su ne wadanda suka ki zuwa domin tabbatar da ikirarin nasu na bogi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here