Matatar Dangote ta rage farashin man fetur

Dangote Refinery

Matatar man fetur na Dangote ta sake rage farashin man fetur zuwa Naira 865 kowace lita.

Rahotanni sun ce matatar man ta sanar da ‘yan kasuwarta da abokan cinikinta wannan ragin a ranar Alhamis.

Wani jami’in matatar man ya tabbatar da rage farashin daga daga 880 zuwa 865 ga manema labarai, inda ya ce matatar man mai zaman kanta ta rage farashin man fetur da naira 15 a safiyar ranar Alhamis.

Ana sa ran gidajen mai kamar MRS Oil & Gas, Ardova Plc, Heyden, da sauran su da suka kulla yarjejeniya ta musamman da matatar Dangote cewa za su rage farashin litar su zuwa kusan Naira 910 daga kusan 925 domin nuna raguwar farashin tsohon man.

Rage farashin da matatar man ta yi ya biyo bayan wata ganawa da wakilan matatar man Dangote suka yi da ministan kudi Wale Edun a ranar Talata.

A karshen taron, gwamnatin ta ce har yanzu kudin danyen mai na Naira yana nan daram, kuma wannan shiri ba na wucin gadi ba ne, illa dai “muhimmin umarnin tsare-tsare da aka tsara don tallafa wa matatun gida mai dorewa.

Gwamnatin ta kuma ce har yanzu shirin na ci gaba da aiki kuma za a ci gaba da aiki da shi, inda ta yi fatali da shawarar da hukumar ta NPL ta yanke a karkashin tsohon shugabanta Mele Kyari wanda ya dauki nauyin shirin.

Labari mai alaƙa: Matatar Mai ta Dangote ta ce ta daina sayar da fetur da Naira

A wani Labari na baya bayan nan….

A wani bangare na yunkurin rage radadin dalar Amurka da kuma tabbatar da daidaiton farashin man fetur, Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a watan Yulin 2024 ta umurci hukumar ta NNPC da ta sayar da danyen mai ga matatar Dangote da sauran matatun man cikin gida a Naira ba wai a kudin kasar Amurka ba.

Sai dai a watan Maris din 2025, Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL) ya ce yarjejeniyar cinikin danyen man da ta ke da nasaba da Naira da matatar man Dangote an tsara shi ne na tsawon watanni shida, inda a watan Maris na 2025 ta kasance ranar karewar wa’adin.

Daga baya, matatar Dangote ta dakatar da sayar da man fetur a Naira na wani dan lokaci, inda nan take farashin man fetur ya tashi daga kusan Naira 860 zuwa kusan 1,000, wanda hakan ya sa masu sayen man suka biya akalla Naira 70 fiye da yadda ake sayan lita guda a kwanakin baya.

Sai dai matatar man ta ce za ta dawo da sayar da kayanta ga kasuwannin cikin gida a Naira da zarar ta karbi danyen mai daga NNPC a Naira.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here