Ministan Ilimi Dr. Tunji Alausa, ya umurci dukkan manyan makarantun gwamnatin tarayya da aka ba su izinin daukar ma’aikata da su tallata guraben aiki da ake da su a bainar jama’a.
A wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Folasade Boriowo, ya fitar a Abuja ga manema labarai a ranar Alhamis, ta ce ministar ya umurci makarantun da su rika tallata guraben aiki a akalla wata jarida ta kasa, ko a shafukansu na intanet, da sauran mujallu na ilimi.
Alausa ya ce umarnin na da nufin tabbatar da tsarin daukar ma’aikata a bayyane, da ba da dama daidai ga duk ‘yan Najeriya da suka cancanta.
Ya tunatar da daukacin manyan makarantun gwamnatin tarayya da su mika bukatunsu na daukar ma’aikata ga ma’aikatar ilimi domin tantancewa daga kwamitin daukar ma’aikata.
Ministan ya kara da cewa “Ma’aikatar ta samar da isassun hanyoyin tabbatar da bin ka’ida kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen sanya takunkumi kan duk wata cibiya da ta ki bin wannan umarnin.”