Gamayyar kungiyoyin farar hula ta Kano CCKCSG, ta yi Allah-wadai da abin da ta bayyana a matsayin yadda rundunar ‘yan sandan Najeriya ke ci gaba da rura rikicin masarautar Kano.
Kungiyar ta bayyana damuwar ta ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba ta hannun shugabanta Nura Idris.
Gamayyar kungiyoyin sun soki ‘yan sanda kan sammacin da suka yi wa Sarki Muhammadu Sanusi na biyu, inda ta bayyana hakan a matsayin rashin mutuntawa da kuma siyasa.
Sammacin, wanda aka ruwaito ya biyo bayan yadda Sarkin ya gudanar da bikin Hawan Eid al-Fitr, wanda ya sa yan sanda suka bukaci ya bayyana a hedkwatarsu da ke Abuja.
Karanta: Gwamnatin Kano ta kaddamar da ingantaccen dakin gwaje-gwaje na sarrafa gurbatar yanayi
Daga baya ‘yan sandan sun janye sammacin bayan da jama’a suka yi ta cece-kuce.
Kungiyar ta kuma yi tsokaci game da kiran da ‘yan sanda suka yi wa Sarki Muhammadu Sanusi na biyu a matsayin “Alhaji Sanusi” a wata takarda da suka fitar a hukumance, inda ta kira hakan da anyi ne da gangan.
Sanarwar ta bukaci ‘yan sanda da su nemi afuwar jama’a tare da bukatar su da su rika kiran Sarkin da muqaminsa da ya dace a duk wani aiki na gaba.
Da ta ke kira da a nuna taka-tsan-tsan kungiyar ta bukaci babban sufeton ‘yan sandan Najeriya da sauran hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya ba ta zama kanwa a rikicin shugabanci da ke faruwa tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero ba.
Gamayyar kungiyoyin ta kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su nemi tattaunawa da sasantawa, inda ta yi gargadin cewa ci gaba da tashe-tashen hankula na iya yin barazana ga zaman lafiyar jihar Kano.
Ta kuma yi alkawarin ci gaba da sanya ido kan lamarin tare da kara daukar mataki idan har ya dace don kiyaye adalci, shugabanci nagari, da kuma kayayyakin tarihi na masarautar Kano.













































