Maishari’a Haleemah Salman ta Babbar Kotun Jihar Kwara ta yanke hukuncin kisa ga mutum biyar da ake zargi da hannu a fashin banki da ya faru a Offa a shekarar 2018, bisa laifin fashi da makami, mallakar bindigogi ba tare da izini ba, da kuma kisan kai.
A cikin zaman yanke hukuncin da ya dauki awa uku da rabi, alkaliyar ta bayyana cewa duk shaidu da aka gabatar sun tabbatar da laifin mutanen.
Wannan fashin ya faru ne a watan Afrilu na shekarar 2018, inda aka kashe mutane fiye da 30, ciki har da ‘yan sanda, sannan aka kwashe makudan kudade daga bankunan garin.
Baya ga hukuncin kisa, kotun ta kuma yanke musu hukuncin zaman shekaru uku a kurkuku saboda mallakar bindigogi ba tare da izini ba.
Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da Ayoade Akinnibosun, Ibikunle Ogunleye, Adeola Abraham, Salahudeen Azeez, da Niyi Ogundiran. Mutum na shida, Michael Adikwu, ya mutu a tsare.