Hedikwatar tsaro (DHQ) ta tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan ikirarin daukar nauyin ‘yan fashi a yankin Arewa maso Yamma na Najeriya.
Daraktan yada labarai na hukumar ta DHQ, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, inda ya tabbatar da cewa hukumomin da abin ya shafa na yin nazari sosai kan lamarin.
Wannan bincike dai ya biyo bayan zargi da kuma tuhume-tuhume da aka yi tsakanin karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, da wanda ya gaje shi a matsayin gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, dangane da zargin samar da kudade na ‘yan fashi da makami a yankin.
A farkon makon nan ne Matawalle ya kalubalanci Lawal da ya rantse da Alkur’ani mai girma, inda ya musanta cewa yana da hannu a daukar nauyin ‘yan bindiga.
Sai dai Lawal ya mayar da martani inda ya bayyana cewa yana da shaidun da ke nuna Matawalle, kuma ya kai karar mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro kuma shugaban kasa Bola Tinubu.
Da aka tambayi Manjo Janar Buba game da yadda sojoji ke da hannu a lamarin, ya kara jaddada cewa hukumomin da suka dace suna gudanar da binciken kuma nan ba da dadewa ba za a yi karin bayani.