Gwamnatin tarayya ta kwace lasisin AIT, Silverbird da sauran tashoshin watsa labarai 50

BREAKING 1 1
BREAKING 1 1

Hukumar kula da kafafen watsa labarai ta kasa, NBC, ta kwace lasisin kafafen watsa labarai na Silverbird TV, AIT, Raypower FM, Rythm FM da wasu saboda rashin sabunta lasisin aikinsu.

Direkta Janar na NBC Mallam Balarabe Shehu Ilelah kuma ya umurci ofisoshinsu na jihohi su yi aiki tare da jami’an tsaro domin tabbatar da cewa an rufe kafafen watsa labaran cikin awa 24, gwamnatin na bin tashoshin kudi har Naira Biliyan 2.66 a cewar sa.

Mataimakin shugaban kasa Buhari na masamman a bangaren watsa labarai, Bashir Ahmad shima ya tabbatar da umurnin rufe tashoshin watsa labaran a shafinsa na Twitter.

A cewarsa, a watan Mayu, hukumar ta wallafa sunayen tashoshin da ba su riga sun sabunta lasisinsu ba aka kuma basu sati biyu idon ba haka ba a kwace lasisin. Ya ce watanni uku bayan fitar da sanarwar, wasu tashoshin ba su biya bashin da ake binsu ba hakan kuma ya saba dokar Act CAP N11, ta Tarayyar Najeriya, 2004, musamman sashi na 10(a) na sashi na uku na dokar.

Da ya ke sanar da janye lasisin, Ilelah ya bawa tashoshin da abin ya shafa awa 24 su rufe.

Ya yi kira ga dukkan tashohin da abin ya shafa su sabunta lasisinsu cikin kwana 30 don gudun kada a hukunta su.

Ya kuma kara kira ga dukkan tashoshin da ke watsa shirye-shiryensu ta intanet su yi rajista da hukumar don kada a katse su. Ya ce ko sun biya bashin da ake binsu, sai sun biya wani kudin cigaba da watsa labarai.

Jerin tashoshin da abin ya shafa sun hada da Zuma FM, Suleja, Niger State, Bomay Broadcasting Service L.td., Kogi, Kwara, Niger, Gombe, Lagos, Osun, Ogun, Ondo da kuma Rivers States Broadcasting Corporations.

Sauran sun hada da Katsina Broadcasting Corporation, Kaduna State Broadcasting Corporation, Jigawa Broadcasting Corporation, Kebbi State Broadcasting Corporation, Zamfara State Broadcasting Corporation,Yobe State Broadcasting Corporation, Imo State Broadcasting Corporation, Anambra State Broadcasting Corporation, Cross River State Broadcasting Corporation, Bayelsa State Broadcasting Corporation, Borno State Broadcasting Corporation da kuma Crowther FM Abuja.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here