Majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da nadin mutane 12 karkashin jagorancin gwamnan babban bankin kasar, Olayemi Cardoso a matsayin mambobin kwamitin da za su kula da harkokin kudi a babban bankin Kasar CBN.
Wannan tabbacin ya zo ne bayan wani rahoton kwamitin kula da harkokin banki da inshora da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi na babban bankin ya gabatar a zaman majalisar da aka yi ranar Alhamis.
Tabbatar da sabbin mambobin MPC ɗin na zuwa ne kwanaki kaɗan kafin taron tsare-tsaren babban bankin na farko karkashin sabon gwamnan bankin.
An tsara taron ne a ranakun 26 da 27 ga watan Fabrairun 2024, mambobin su ne:
1. Olayemi Cardoso – Shugaba
2. Muhammad Sani Abdullahi – Mamba
3. Bala M. Bello – Mamba
4. Emem Usoro – Mamba
5. Philip Ikeazor – Mamba
6. Lamido Yuguda – Mamba
7. Jafiya Lydia Shehu – Mamba
8. Murtala Sabo Sagagi – Mamba
9. Aloysius Uche Ordu – Mamba
10. Aku Pauline Odinkemelu – Mamba
11. Mustapha Akinwumi – Mamba
12. Bandele A.G. Amoo – Mamba
A watan Nuwambar 2023, Cardoso wanda shugaba Tinubu ya naɗa a matsayin gwamnan CBN a watan Satumba na 2023, ya ce taron na MPC bai yi tasiri a karkashin magabacinsa Godwin Emefiele ba.