‘Yan ta’adda sun kashe mutane 3 tare da yin garkuwa da was da dama a jihar Neja

B51A3648 BE79 4C21 82F5 668DBEC8B29E
B51A3648 BE79 4C21 82F5 668DBEC8B29E

Wasu ‘yan ta’adda sun kashe mutane uku a unguwar Anguwan-Toma da ke karamar hukumar Munya a jihar Neja.

Anguwan-Toma tana da nisan kilomita 2 daga Sarkin Pawa, hedkwatar karamar hukumar Munya, da hanyar da ta hada jihar Neja zuwa titin Kaduna.

Wani mazaunin yankin, Shehu Abubakar, ya ce an kuma yi garkuwa da mutane da dama a harin da aka kai a daren ranar Litinin.

Ya ce daukin gaggawar da jami’an tsaro musamman sojoji suka yi, ya ceci sauran al’ummomin yankin daga harin.

Sai dai ya ce ‘yan ta’adda sun yi wa shaguna a Zazzaga fashi inda suka kwashe kayan abinci.

Ya ce ‘yan ta’addan sun kuma tare hanyar Sarkin Pawa zuwa Minna a yammacin ranar Talata tare da yin fashin shaguna tare da sace kayan abinci.

An tattaro cewa ‘yan ta’addan sun kuma mamaye Nasko, hedikwatar karamar hukumar Magama, inda suka yi awon gaba da shanu a yammacin ranar Litinin.

Kwamishinan kananan hukumomi, masarautu da tsaron cikin gida na jihar Neja, Emmanuel Umar, ya tabbatar da faruwar harin amma bai iya bayyana adadin wadanda suka rasa rayukansu ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Ya ce, “An yi awon gaba da shanu a Nasko, kuma mun aika da jami’an tsaro su tare hanyar tserewa tare da kama su.

Kamar yadda muke magana yanzu, wasu daga cikin shanun sun fara komawa baya yayin da jami’an tsaro ke bin sahun barayin.”

Ya ce jami’an tsaro kuma suna mayar da martani kan lamarin a karamar hukumar Munya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here