Hukumar NiMet ta yi hasashen samun Ruwa da tsawa

Rainfall (1)

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet, ta yi hasashen cewa za a yi tsawa da ruwan sama daga yau Asabar zuwa Litinin a fadin Najeriya.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wani rahoto da ta fitar ranar Juma’a a Abuja, wanda ya yi hasashen cewa, za a yi tsawa da ruwa a sanyin safiyar ranar Asabar a wasu sassan jihohin Taraba da Kebbi da Zamfara da Kaduna da Adamawa.

Haka kuma hukumar ta ce, ana sa ran cewa za a yi tsawa da ruwan sama a sassan jihohin Kebbi da Taraba da Zamfara da Borno da Kaduna da Sokoto da Gombe  da Bauchi.

A yankin Arewa ta Tsakiya ana sa ran za a yi tsawa da sanyin safiya a sassan jihohin Benue da Plateau da Niger da Babban Birnin Tarayya Abuja da jihar Nasarawa.

“A washegari, ana hasashen samun tsawa da ruwan sama a sassan babban birnin tarayya Abuja da Niger da Nasarawa da Benue da Kwara da Kogi da Filato.

NiMet ta kuma yi hasashen samun tsawa sosai da mamakon ruwan sama a jihohin Imo da Enugu da Abia da Ebonyi da Anambra, sai Ondo da Oyo da Osun da Ogun da kuma Ekiti da Edo da Delta da Cross River da Akwa Ibom sai Bayelsa da kuma jihar Rivers.

Hukumar ta yi hasashen cewa za a yi tsawa a safiyar ranar Lahadi a wasu sassan jihohin Kaduna da Kebbi da Adamawa da Taraba a yankin Arewa.

Haka kuma, ta yi hasashen yin tsawa da ruwan sama a wasu sassan jihohin Taraba da Adamawa da Kebbi da Kaduna da Zamfara da Gombe da Bauchi a yammacin ranar.

Haka dai, hukumar NiMet ta yi hasashen samun gajimare da daga bisani zai koma washewar gari da sanyin safiya a jihohin  Kogi da Kwara da Plateau da Neja da Nasarawa da Benue da kuma Birnin Tarayya Abuja.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here