Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da aikin yashe magudanan Ruwa

WhatsApp Image 2025 06 13 at 12.26.45 750x430

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da aikin share magudanan ruwa na shekara shekara a Shatale-talen titin Baban Gwari yankin da ake fama da ambaliyar ruwa a tsakiyar birni.

WhatsApp Image 2025 06 13 at 12.26.47 768x576

Ɗaukar matakin shi ne domin magance matsalar ambaliyar ruwa da tabbatar da tsaftar muhalli a daminar bana.

WhatsApp Image 2025 06 13 at 12.44.15 768x575

SolaceBase ta ruwaito cewa yayin ƙaddamar da aikin a ranar Juma’a, kwamishinan muhalli da sauyin yanayi, Dakta Dahiru Muhammed Hashim ne ya jagoranci aikin inda ya bayyana shi a matsayin wani muhimmin mataki na dakile illolin da ke tattare da toshe hanyoyin magungunan ruwa.

WhatsApp Image 2025 06 13 at 12.26.48 768x576

“Wannan ba wai kawai wani aikin gwamnati bane,” in ji Dr. Hashim. “Wannan wata alama ce a fili ta kudurinmu na samar da ingantaccen tsarin kula da muhalli da kuma daukar matakai gabanin kankamar damina don ganin an gyara magudanan Ruwa.

Shatale-talen na Baban Gwari, da aka, kaddamar da aikin waje ne da aka dade ana fama da ambaliyar ruwa, wanda hakan ke shafar lafiya, da kuma zirga-zirgar makwabtan yankin har ma da masu bin hanyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here