Yarima Charles ya gaji marigayiya Elizabeth

FB IMG 16626657908852567
FB IMG 16626657908852567

Rahotanni da su ke fito wa daga Masarautar Buckingham sun nuna cewa Yarima Charles ya zama Sarkin Ingila, bayan rasuwar mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth ta biyu.

Da yammacin Alhamis ɗin nan ne Elizabeth ta mutu tana da shekaru 96 a duniya.

Jaridar AFP ta rawaito cewa, rasuwar ta ta ke da wuya, sai a ka sanar da Charles, wanda shi ke babban ɗanta, mai shekaru 73 da haihuwa, a matsayin wanda zai gaje ta.

Sarauniya Elizabeth dai ita ce mafi daɗewa wa a kan karagar mulkin, inda ta shafe shekaru 70 ta na mulki

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here