Majalisar wakilai ta amince da Naira Tiriliyan 54.99 a matsayin kasafin kudin 2025

Reps new

Majalisar wakilai ta amince da kudirin kasafin kudin shekarar 2025 na naira tiriliyan 54 da biliyan 99 a zamanta na yau Alhamis.

A makon da ya gabata ne shugaban kasa Bola Tinubu ya kara kasafin kudin shekarar 2025 daga Naira Tiriliyan 49 da biliyan 7 zuwa Naira Tiriliyan 54 da biliyan 2, inda ya nemi amincewar majalisar dattawa da ta wakilai.

Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar, Abubakar Bichi, a lokacin da yake gabatar da kudirin dokar don tantancewa, ya bayyana cewa, kwamitin ya gana da tawagar shugaban kasa kan tsara tattalin arziki domin ci gaba da tattaunawa kan hasashen kudaden shiga da kuma yadda za a kashe kudaden kasafin kudin shekarar 2025.

Karanta: Tinubu ya nemi majalisa ƙara yawan kuɗin kasafin 2025 zuwa Tiriliyan 54.2

A cewarsa, an gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2025 a makare, idan aka kwatanta da na 2024.

Ya bukaci hukumar zartaswa da ta gabatar da kasafin kudi na gaba ga Majalisar Dokoki ta kasa nan da watanni uku kafin shekarar kudi ta gaba, don kiyaye tsarin kasafin kudin Janairu zuwa Disamba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here