Zargin karkatar da Naira Biliyan 2.5: Kotu ta sallami tsohon shugaban NBC

Kawu Moddibo

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja a ranar Alhamis, ta sallama tare da wanke tsohon Darakta-Janar na hukumar kula da kafafen yada labarai ta Kasa (NBC), Ishaq Kawu daga zargin almundahanar Naira biliyan 2da Miliyan 5.

Da take yanke hukunci, Mai shari’a Folashade Giwa-Ogunbanjo, ta ce hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta kasa tabbatar da zargin da take yiwa Kawu da sauran wadanda ake tuhuma.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN, ya ruwaito cewa an tuhumi Kawu da wasu a kan wasu laifuka biyar da aka yi wa kwaskwarima na karkatar da kudaden da aka tanada na tsarin amfani da (DSO) da gwamnatin tarayya ta bullo da shi.

Karin labari: Zargin almundahana: Kotu ta sanya ranar da za ta saurari shari’ar Ganduje da matarsa da wasu 6.

An gurfanar da Kawu ne a shekarar 2019, tare da Lucky Omoluwa da Dipo Onifade, shugaban kamfanin Pinnacle Communications Limited da kuma babban jami’in gudanarwa, bisa zarginsu da hannu wajen karkatar da tallafin na Naira biliyan 2 da miliyan 5.

ICPC ta yi zargin cewa tsohon babban daraktan NBC ya yi wa ministan yada labarai da al’adu shigo-shigo ba zurfi don amincewa da biyan Naira biliyan 2 da miliyan 5 ga kamfanin Pinnacle Communications Limited, wani kamfani mai zaman kansa mallakin abokinsa, Omoluwa wanda shi ne ake tuhuma na 3.

A cewar hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa, Omoluwa, wanda kamfaninsa bai cancanci samun irin wannan tallafin ba, daga bisani ya mika zunzurutun kudi har naira miliyan 537.25 daga cikin naira biliyan 2.5 ga wani ma’aikacin ofishin canji na dala, shi kuma ya kai kudin dala ne ga wanda ake kara na 3 (Omoluwa) a gidansa da ke Kaduna.

Ko da yake a baya hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta shigar da kara a kan wadanda ake tuhuma da laifuka guda 12, amma daga baya an yi mata kwaskwarima kan tuhume-tuhume biyar.

Laifin, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ce ya sabawa sashe na 26(1) (c) kuma ana hukunci a karkashin sashe na 19 na dokar cin hanci da rashawa da sauran laifuka masu alaka, 2000″(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here