Kungiyoyin da ke rajin ci gaban al’umma a Kano sun taya Jihar murna bisa samun gagarumar nasara a jarabawar kammala sakandare ta ƙasa ta shekarar 2025 (NECO), inda fiye da dalibai 68,000 suka samu sakamako mai kyau na aƙalla darussa biyar ciki har da Turanci da Lissafi.
Wannan ya sa Kano ta zama jiha ta farko a jerin jihohin Najeriya.
A wata sanarwa da suka fitar ranar Alhamis, kungiyoyin sun danganta nasarar ga jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda suka yaba da ƙudurin gwamnatinsa na ƙara kuɗin ilimi, ɗaukar malamai ƙwararru, da tallafawa ɗalibai marasa ƙarfi.
Sai dai duk da wannan ci gaba, kungiyoyin sun nuna damuwa kan matsalolin da ake fama da su a matakin firamare kamar cunkoson ɗalibai a aji, rashin tsafta a makarantu da ƙarancin malamai ƙwararru.
Sun gargadi cewa waɗannan matsaloli na iya kawo cikas ga ci gaban da aka samu idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba.
Rahoton SolaceBase ya nuna cewa, kungiyoyin sun bayar da shawarwari guda shida don magance matsalolin, ciki har da yin cikakken binciken gina makarantu, ɗaukar malamai 25,000, da kuma ƙarfafa tsarin shugabanci da sa ido ta hanyar fasahar zamani don tabbatar da gaskiya da ɗawainiya.
Kungiyoyin sun kuma roƙi gwamnatin Kano da ta zurfafa a gyaran tsarin ilimi tare da daidaita manufofi da ka’idojin cikin gida da na ƙasa da ƙasa, tare da jaddada cewa ingantaccen ilimi dole ne ya fara daga matakin firamare.
Sanarwar ta samu sa hannun shugabanni da kungiyoyi 22 na farar hula, ciki har da ƙungiyar ci gaban Al’ummar Wuro (WDCN), Cibiyar Ƙarfafa ’Yancin Dan Adam da ci gaban Jama’a (CEFSAN), Cibiyar Afirka ta Bincike da ci gaban fasaha (Afri-CIRD), Ƙungiyar wayar da kan matasa, Ƙungiyar farar hula ta sulhu da rikice-rikice a Najeriya (CS-CRIN), Ƙungiyar haɗin gwiwa ta Aiki (JAF), Ƙungiyar Haɗin kai don Dimokuraɗiyya (UAD), da cibiyar kare Adalci, gaskiya da ƴancin dan Adam da sauran su.
Kungiyoyin sun sha alwashin ci gaba da mara wa gwamnati baya ta hanyar bayar da tallafin fasaha, wayar da kan al’umma, da kuma sa ido domin tabbatar da cewa kowanne yaro a Kano ya samu ingantaccen ilimi mai adalci da daidaito.













































