Hukumar kula da hasashen yanayin ruwan sama ta kasa NIHSA ta ce al’ummomi 1,249 a cikin jihohi 30 da babban birnin tarayya na cikin hadarin fuskantar ambaliya.
Hukumar ta kara da cewa al’ummomi 2,187 a cikin kananan hukumomi 293 za su fada cikin matsakaitan hadarin ambaliyar ruwa.
Da yake jawabi a Abuja ranar Alhamis yayin kaddamar da hasashen ambaliyar ruwa na shekara ta 2025, ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli Joseph Utsev, ya ce har yanzu ambaliyar ruwa na daya daga cikin bala’o’i mafi muni a Najeriya, inda sauyin yanayi ke haddasa ta, baya ga yadda yake kara yawaita.
Utsev ya ce jihohin da za su yi fama da matsalar ambaliya sun hada da: Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross-River, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Rivers, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara da kuma babban birnin tarayya.
Al’ummomi 1,249 a kananan hukumomi 176 na kananan hukumomi 176 a fadin jihohi 30 da babban birnin tarayya Abuja sun fada cikin yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa a bana, yayin da karin al’ummomi 2,187 a cikin kananan hukumomi 293 ke fuskantar hadarin ambaliyar ruwa,” in ji Utsev.
Ministan ya kuma sanar da kaddamar da ayyuka da dama da suka hada da shirin inshorar ambaliyar ruwa na kasa (NFIP) – shirin inshora irinsa na farko na kare matsugunan gidaje, gonaki, da dabbobi inda jihohin Kogi da Jigawa suka kasance a matsayin na gwaji.
Sauran sun hada da hadaddiyar aikin kirkiro da juriyar yanayi (I-CRIP) da nufin inganta samar da abinci, samar da makamashi, da kuma amfani da albarkatun ruwa ta hanyar dabarun da suka dace da yanayi, da aikin NigerFLOOD – don magance ambaliyar ruwa da sarrafa kogi, da dai sauransu.
A shekarar 2024, ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane 321, ta kuma shafi sama da mutane miliyan 1.37, tare da raba sama da 740,000 da muhallansu a fadin Najeriya.