Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo a ranar Alhamis ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar sun kafa kwamitin bincike kan kisan da aka yi wa mafarauta a garin Uromi da ke Edo.
Okpebholo ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin wata babbar tawaga daga jihar Kano karkashin jagorancin mataimakin gwamna Aminu Abdulsalam Gwarzo a Benin.
Ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bai ji dadin faruwar wannan mummunan lamari ba, kuma ya jajirce wajen tabbatar da tsaron dukkan ‘yan kasa.
“Shugaban kasa ya kuduri aniyar gano tushen wannan lamari, muna son a samu mafita mai dorewa da adalci ga duk wadanda abin ya shafa.
A cewar Okpebholo, Edo gida ce ga masu son zaman lafiya.
A nasa jawabin kwamared Abdussalam Gwarzo ya nuna godiya ga Okpebolo bisa ziyarar da ya kai jihar Kano a baya da kuma kokarin da ya yi a lokacin rikicin.
“Ziyarar ta mu ita ce mu mika godiya ta musamman kan yadda kuka shiga cikin lumana a lokacin rikicin Uromi da kuma hadin kan ku da mutanen Kano,” in ji Gwarzo.
“Jihar Kano ta kafa wani kwamiti domin tantance sunaye, lambobi, dangi, da wadanda suka tsira, mun zo nan ne domin gabatar da rahoton karshe a hukumance.
“An rasa rayuka goma sha shida—wadanda aka kashe daga kananan hukumomi biyar a Kano.
Daga baya Okpebholo da tawagar Kano sun ziyarci Uromi, inda suka gana da al’ummar Hausawa da lamarin ya shafa. (NAN)