
Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar IS ne a yammacin Afirka sun kashe wani jami’in dan sanda mai suna Sunday Pius da ke karamar hukumar Marte a jihar Borno.
Haka kuma, ‘yan sanda biyu sun samu raunuka.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, ASP Kenneth Daso ne ya tabbatar da kisan DPO a ranar Talata a Maiduguri.
Karin labari: Hukumar NEDC ta kara himmatuwa don inganta ilimi a jihar Gombe
Daso ya ce, “Mun samu kiran waya a yau cewa ‘yan ta’adda sun kashe daya daga cikin jami’an mu, Sufeto Sunday Pius, jami’in ‘yan sanda reshen jihar New Marte, da yammacin ranar Litinin da ta gabata.
“Koda yake, tawagarmu da aka tura zuwa Marte har yanzu ba su zo da cikakkun bayanai ba, amma da zaran na samu cikakkun bayanai, zan ba wa manema labarai daidai.”
Karin labari: ‘Yan bindiga sun kashe sama da mutum 40 da jikkata wasu da dama a Filato
Sai dai an samu labarin cewa ISWAP din ta kutsa kai cikin yankin Marte da misalin karfe 7:30 na yammacin ranar Litinin inda suka farwa wani ma’aikacin lafiya da ya yi sa’a ya tsere.
An bayyana cewa ma’aikacin lafiyar ya garzaya ofishin domin sanar da ‘yan sanda, DPO din ya bi sawun ‘yan ta’addan, amma abin takaici sai suka yi wa tawagar ‘yan sanda kwanton bauna.
Garin Marte da ke iyaka da yammacin gabar tekun Chadi da jamhuriyar Kamaru, kuma mai tazarar kilomita 120 daga Maiduguri ya sha fama da munanan hare-hare daga ‘yan ta’adda, tare da raba mazauna garin da yawa, kafin daga bisani sojoji su ‘yantar da shi.












































