Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Wasu ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Zurak da ke gundumar Bashar, a ƙaramara hukumar Wase, ta jihar Filato, inda suka kashe sama da mutum 40 da suka haɗa da ‘yan sa kai.
Rahotanni na cewa gungun ƴan bindigar sun kai harin ne da yamma wajen ƙarfe 5:00pm ranar Litinin a lokacin jama’a na gudanar da harkokinsu.
Al’ummar ƙauyen sun ce ba su iya bayar da rahoton harin ba saboda rashin kyakkyawar hanyar sadarwa a yankin.
Karin labari: Yanzu-yanzu: CBN ya kara kudin lamuni
Wani daga cikin mutanen garin ya ce ƴan bindigar sun yi musu dirar mikiya ne a kan babura ɗauke da manyan makamai inda nan da nan suka riƙa harbin kan mai uwa da wabi.
Bayanai sun nuna cewa ƴan bindigar sun kashe mutum sama da 40, yayin da suka raunata wasu da dama, kuma suka rika cinnawa gidaje wuta.
Mutane sun gudu zuwa cikin daji da wasu garuruwan da ke maƙwabtaka da su domin tsira.
Karin labari: Majalisar Osun ta ba da shawarar karin albashi ga masu rike da mukamin siyasa
Kakakin gwamnan jihar ta Filato, Mista. Gyang Bere, ya tabbatar da lamarin, sai dai bai bayyana yawan mutanen da lamarin ya rutsa da su ba.
Hukumomi sun ce an tura jami’an tsaro domin bin sawun ƴan bindigar.